A karon farko cikin shekaru biyar, firaministan India Narendra Modi zai gana da takwaransa na Chaina Xi Jinping a Larabar nan a birnin Kazan na kasar Rasha, don tattauna batun warware takaddamar da ke tsakaninsu game da kan iyaka.
Karin bayani:Putin ya karbi shugabanni a taron kolin BRICS
Ganawar ta su na zuwa ne a daura da taron kungiyar kasashen BRICS masu habakar tattalin arziki cikin hanzari da ke shiga rana ta biyu da farawa, kamar yadda wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen India Vikram Misri ya sanar.
Karin bayani:Ana shirin bude taron kasashen BRICS a Rasha
Zaman tankiya tsakanin kasashen biyu ya fara zafi ne sakamakon gwabzawar da dakarun tsaronsu suka yi da juna a shekarar 2020, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar sojojin India 20 da kuma guda 4 na Chaina.