Rahoto ya fito karara da hadarin da rayuwar al'ummar duniya ke ciki a yanzu. Mutum akalla miliyan tara ne suka yi mutuwar bakatatan a sakamakon cututtuka masu nasaba da shakar gurbatacciyar iska a shekarar 2019 fiye da yadda lamarin ya ke a can baya.
Rahoton ya kara da cewa, gurbatacciyar iska na lakume rayuka fiye da rikicin yaki da aiyukan ta'addanci dama annoba cututtuka kamar tarin fuka da zazzabin malariya dama HIV ko kayan maye da sauransu.
Kasashe masu tasowa da matalauta su suka fi shan wuya a sakamakon yawan dogaro da suke yi kan makamashin man fetur don bunkasa tattalin arzikinsu. Rahoton ya kara baiyana illolin da gurbatacciyar iska ke haddasawa da masana ke cewa ya zarta duk yadda ake hasashe.