Antonio Guterres ya ce lamarin na kara kazanta inda a yanzu haka sama da mutum biliyan daya da rabi a fadin duniya ke fuskantar barazanar yunwa. Ya baiyana hakan ne yayin da yake gabatar da rahoto a karo na biyu a game da rikicin na kasashen Rasha da Ukraine.
Ya kara da cewar babban abin da ke kokarin jefa duniya cikin mawuyacin hali na yunwa a wannan shekarar shi ne rashin bada damar fitar da abinci da Rasha ke yi. Guterres ya ce shekarar da ke tafe ka iya zama mafi muni a saboda da rashin abinci.
Babban jami'in na Majalisar Dinkin Duniya cikin tattausan lafazi ya bukaci kawo karshen yakin wanda ya ce ci gaba da shi ka iya haifar da wata matsalar da za a yi da na sani.