Hukumar da ke kula da makashin nukiliya a duniya, IAEA, ta sanar a wannan Litinin cewa kasar Iran ta mallaki makamashin uranium da ya haura sau 18 na adadin da yarjejeniyar Iran da manyan kasashen duniya ta 2015 ta yi tanadi.
A cikin sabon rahoton da hukumar ta MDD ta fitar ta ce hukumomin Iran sun azurta kansu da sinadarin uranium da ya kai nauyin kilogiram kusan 4000 a maimakon kilogiram 300 da yarjejeniyar nukiliyar Iran din ta amincewa kasar.