IAEA: Hari a tashar nukiliyar Ukraine na da hadari

IAEA: Hari a tashar nukiliyar Ukraine na da hadari
Hukumar da ke kula da makamashin nukiliya ta Duniya IAEA ta yi kira a kan hadarin da ke tattare da harin da ake kai wa a kusa da tashar makamashin nukiliyar kasar Ukraine da ke Zaporizhzhia.

A wani zama da ya gudana a jiya alhamis, tsakanin hukumar da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, shugaban hukumar ta IAEA Rafael Grossi ya ce akwai bukatar gudanar da bincike a kan sanin takamaimai me ke faruwa a wannan tashar.

Grossi ya kuma kara da nuna girman hadarin da ke tatare da kai hari a tasahr da ka iya shafar duka nahiyar Turai ba ma kawai ga kasahen da ke rikici da junansu ba.

Shugaban kasar Ukraine Volodmyr Zelensky ya bukaci kasashen yamma da su dauki mataki na gaggawa domin korar dakarun Rasha a kusa da wannan tashar da ke karkashin ikon sojojin na Moscow.

Tuni dai mambobin kwamitin sulhu suka amince da daukar mataki da ake fatan ya kawo karshen mamaya a kusa da wannan tasha da ke zama mafi girma a nahiyar Turai.
 


News Source:   DW (dw.com)