Kungiyar kare hakkin 'dan adam ta Human Rights Watch ta zargi Isra'ila da aikata laifukan yaki da kuma kisan kare dangi a Gaza, tare da umartar mazauna yankin barin muhallansu ala tilas.
Karin bayani:Yariman Saudi Arebiya ya bukaci gaggauta kawo karshen yakin Gaza da na Lebanon
Rahoton da kungiyar ta fitar mai shafuka 172, ya nuna alkaluman da ta tattara a matsayin hujjojin da za su tabbatar da ikirarinta, la'akari da irin ayyukan da dakarun Isra'ila ke gudanarwa a yankin na Falasdinawa, kamar yadda babbar jami'a a kungiyar Nadia Hardman ta tabbatar.
Karin bayani:Kasashe 52 na son MDD ta haramta wa Isra'ila sayen makamai
Wata kidddiga da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta nuna cewa Falasdinawa kusan miliyan biyu ne suka tsere daga gidajensu a zirin Gaza, daga watan Oktoban bara zuwa na bana, kuma yankin na Gaza na da mutane miliyan biyu da dubu dari hudu.