Huldar Masar da Turkiyya

Kasashen Masar da Turkiyya dai su ne kusan suka fi karfin fada a ji a siyasar Gabas ta Tsakiya musamman rikicin Palasdinawa da Isra'ila. Masu lura da siyasar kasashen biyu suka ce akwai matukar inganta hulda tsakanin Turkiyya da Masar a baya-bayannan, inda wasu ke cewa ziyarar Al-Sisi ya zo Turkiyya ne kawai don kara tabbatar da dinke wannan kawancen da kasashen biyu suka riga suka cimma. An dai dauki sama da shekaru goma da raba gari tsakanin kasashen biyu, har sai a watan Febrairun bana da shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci Alkahira, wanda a nan ne shugabannin biyu suka ce sun shafi matsayinsu na baya kuma an bude sabon babi na hulda tsakanin kasashen biyu. Turkiyya dai ta kasance kasar da jami'an kungiyar Mulism Brotherhood ke fakewa, kungiyar da ta yi mummunar adawa da gwamnatin Al-Sisi bayan da ya kifar da gwamnatin Mohammed Mursi.


News Source:   DW (dw.com)