Kasashen Masar da Turkiyya dai su ne kusan suka fi karfin fada aji a siyasar Gabas ta Tsakiya musamman rikicin Palasdinawa da Isra'ila. Masu lura da siyasar kasashen biyu suka ce akwai matukar inganta hulda tsakanin Turkiya da Masar a baya-bayannan, inda wasu ke cewa ziyarar Al-Sisi ya zoTurkiyya ne kawai don kara tabbatar da dinke wannan kawancen da kasashen biyu suka riga suka cimma. An dai dauki sama da shekaru goma da raba gari tsakanin kasashen biyu, har sai a watan Febrairun bana da shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci Alkahira, wanda a nanne shugabannin biyu suka ce sun shafi matsayinsu na baya kuma an bude sabon babi na hulda tsakanin kasashen biyu. Turkiya dai ta kasance kasar da jami'an kungiyar Mulismbrodahood ke fakewa, kungiyar da ta yi mummunan adawa da gwamnatin Al-Sisi bayan da ya kifar da gwamnatuin Mohammed Mursi.
News Source: DW (dw.com)