Hukumar raya kasashe ta Amurka USAID na shirin rufewa

 Attajirinmai kudin na duniya, Elon Musk, wanda shugaba Donald Trump ya dorawa alhakin kawo sauye-sauye, a gwamnatin tarrayar.

Ya ce  hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) da ke kula da taimakon biliyoyin daloli a duniya za ta rufe, wani mataki na musamman da masu sukarsa suka dauka ya sabawa doka.

Hamshakin attajirin ya ce yana da cikakken goyon bayan shugaban na   Amurka, wanda shi da kansa ya fada a ranar Lahadin da ta gabata cewa, hukumar ta USAID,wasu gungun mahaukata masu tsattsauran ra'ayi ke tafiyar da harkokinta.

 Hasali ma, ma'aikatan hukumar da ke gudanar da shirye-shiryen agaji a wasu kasashe 120, an umarcesu ta hanyar imel da kada su je ofisoshinsu a yau Litinin.

Hukumar mai zaman kanta da aka kirkira ta hanyar dokar Majalisar Dokokin Amurka, tana da kasafin kudi na dala biliyan 42.8, don taimakon jin kai da taimakon raya kasa a duk a  fadin duniya.

 


News Source:   DW (dw.com)