Harin na wannan safiyar ya sauka a kan wasu iyakokin sojin Isra'ila 11 da ke arewacion kasar, a cewar kungiyar wannan shi ne mataki na farko na ramuwar kisan babban kwamandansu da Isra'ilan ta yi a watan jiya a Beirut.
A gaba a yau ne firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai gana da majalisar ministocinsa a kan matakin da za su dauka.
Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce za su yi duk mai yiwuwa na ganin sun kare kansu daga duk wani harin Hizbullah.
Tuni mahukuntan Isra'ila suka karkatar da ma dakatar da sauka da tashin jirage daga babban filin jirgin sama na kasa da kasa na Ben Gurion.
Kungiyar Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran ta sha yin musayar wuta da sojojin Israila a wani mataki na nuna goyon baya ga Hamas a yakin da take yi da Isra'ila tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoban bara.