Kungiyar Hezbollah ta tabbatar da mutuwar jagoranta Hassan Nasrallah bayan gumurzun da kungiyar ta yi da dakarun Isra'ila a kudancin Beirut a jiya Juma'a har zuwa yau Asabar.
A wata sanarwa da kungiyar ta Hezbollah ta fitar ta ce Nasrallah ya yi 'shahada', kuma dakarun kungiyar za su dora daga inda ya tsaya wajen goyon bayan al'ummar Falasdinu tare kuma da ci gaba da kai hare-hare kan Isra'ila.
Ma'aikatar lafiyar Lebanon ta ce mutane shida sun mutu a harin na jiya Juma'a yayin da mutane 91 suka samu munanan raunuka, tare kuma da ruftawar wasu manyan gine-gine guda shiga. Sanarwar ta kara da cewa harin ya halaka kwamandan Hezbollah da ke kula da shiyyar kuduncin Beirut Ali Karki kamar yadda Isra'ila ta tabbatar da mutuwarsa. A gefe guda babban hafsan tsaron Isra'ila Janar Herzi Halevi ya ce dakarun Isra'ila za su ci gaba da nausawa Lebanon har sai hakarsu ta cimma ruwa dangane da hare-haren da suka tsara kaddamarwa kan Lebanon.
Sama da mutane 750 ne suka mutu yayin da wasu dubban suka jikkata, tun bayan kaddamar da hare-haren na dakarun Isra'ilan kan mayakan Hezbollah.