Kungiyar Hezbollah ta sanya ranar da za ta gudanar da jana'izar ban girma ta tsohon shugaban kungiyar Hassan Nasrallah, watanni biyar bayan da dakarun sojin Isra'ila suka halaka shi a yayin wani farmaki da suka bai kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon.
Karin bayani: Isra'ila ta zargi Hezbollah da kaiwa MDD hari a Lebanon
Sojojin Isra'ila sun kashe Nasrallah a ranar 27 ga watan Satumbar 2024, inda aka binne shi a asirce a wani kebantaccen wuri ba tare da an gudanar da babban taro ba.