Hezbollah ta kai mummunan hari kan sansanin sojin Isra'ila

Harin da aka kai wa sansanin horar da sojoji na Binyamina da ke kusa da Haifa, na zama hari mafi muni da aka kai a sansanin sojin Isra'ila tun bayan da rikici ya rincabe tsakanin Isra'ilar da kungiyar Hezbullah ta kasar Lebanon. Hezbolla ta ce ta kai harin ne a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da Isra'ila ta kai mata ciki har da ta kai kan ma'aikatar kiwon lafiya na Lebanon, wanda ya yi sanadin rayukan mutane 22 a tsakiyar Beirut a ranar Alhamis din data gabata.

Karin bayani: Jamus ta yi kiran a dakatar da rikicin Isra'ila da Hezbollah

A cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar Hezbollah ta gargadi Isra'ila da cewa, abun da ta gani a kudancin Haifa, somin tabi ne kan abun da za ta gani a nan gaba, idan ta cigaba da wuce gona da iri kan al'ummarta.

 


News Source:   DW (dw.com)