Hausawan Sudan sun yi tir da zubar da jini

Hausawan Sudan sun yi tir da zubar da jini
Daruruwan Hausawa sun taru a birnin Khartoum a wannan Talata domin yin tir da rigingimun kabilanci tsakaninsu da kabilar Bartis wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 79 a karshen makon jiya.

Galibin masu zanga-zangar na dauke da allunan da ke neman a kawo karshen kashe-kashen Hausawa, yayin da wasu ke jinjina wa wadanda tashin hankalin ya ritsa da su. Wannan rikici kan kasa tsakanin Hausawa da kabilar Bartis- ya barke ne a ranar Litinin din da ta gabata a jihar Blue Nile da ke kan iyakar Sudan da kasar Habasha.

Duk da cewa hankali ya kwanta a wannan yanki, amma rikicin ya bazu zuwa wasu jihohi da dama na Sudan da suka hada da Kassala da ke Arewa, inda a ranar Litinin dubban Hausawa suka kona wasu gine-ginen gwamnati. Dama dai rikicin ruwa da filayen noma sun jima suna sanadin mutuwar daruruwan mutane a kasar Sudan.

 


News Source:   DW (dw.com)