Hasashe ya nuna tattalin arzikin Ukraine ka iya habaka

Hasashen bankin sake gina kasashe da ci gaba na nahiyar Turai ya yi nuni da cewa, tattalin arzikin kasar Ukraine zai habaka da kashi biyar nan da shekarar 2026 idan har aka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yakin kasar.

Bankin da ke da mazauni a birnin Landan, ya yi bita kan tattalin arzikin kasar ne yayin da Ukraine din ke fama da hauhawar farashin kaya sakamakon hare-haren da Rasha ta kaddamar kan cibiyoyin makamashinta. A cewar bankin, ana sa ran tattalin arzikin Ukraine ya habaka da kashi 3.5 a wannan shekarar kafin ya haura zuwa kashi biyar a shekarar 2026.

A yanzu shugaban Amurka, Donald Trump na ta kokarin ganin yadda zai kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru uku ana gwabzawa.

   


News Source:   DW (dw.com)