Harin Rasha ya kashe babban manomi a Ukraine

Harin Rasha ya kashe babban manomi a Ukraine
Wani kazamin harin dakarun Rasha a tashar jiragen ruwa a birnin Mykolaiv da ke kudancin Ukraine, ya yi sanadiyyar mutuwar daya daga cikin masu manyan kamfanin noma da fitar da hatsi a kasar.

Nibulon wanda ke da hedkwatarsa a Mykolaiv, birni mai mahimmanci wanda ke iyaka da yankin Kherson da Rasha ta mamaye ya shahara wajen samarwa da fitar da alkama da masara kuma yana da nasa jiragen ruwa da tashar jirgagen ruwa. Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya bayyana mutuwar Vadatursky a matsayin babban rashi ga daukacin kasar yana mai cewa dan kasuwan ya kasance yana ci gaba da gina kasuwar hatsi ta zamani.

An kuma jikkata mutane uku a harin da aka kai a Mykolaiv, kamar yadda magajin garin Oleksandr Senkevych ya shaidawa gidan talabijin na Ukraine, ya kara da cewa makamai masu linzami 12 sun afkawa gidaje da cibiyoyin ilimi. Tun da farko ya bayyana hare-haren a matsayin "watakila mafi karfi" a birnin da aka kwashe tsawon watanni biyar ana yakin.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da jirgin ruwa dauke da hatsi ya bar tashar jiragen ruwa ta Odessa na kasar Ukraine a karon farko tun bayan fara yakin, Ukraine da Rasha sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya don fitar da hatsi daga tashar jiragen ruwa uku na tekun Bahar Maliya. Kasashen biyu sun kasance manyan masu samar da kayan abinci a duniya kafin Rasha ta kaddamar da mamayar a watan Fabrairu.


News Source:   DW (dw.com)