Bama-bamai biyu kira gargajiya sun fashe a gaban makarantar Abdul Rahim Shahid da ke cikin unguwar Dasht-e Barchi a yammacin birnin na Kabul wanda nan take yara 6 suka mutu kana wasu 11 suka jikkata. Unguwar galibi mazaunanta tsiraru ne 'yan kabilar Hazaras 'yan Shi'a wadanda suka dade suna fuskantar wariya a kasar ta Afghanistan. Tun da kungiyar Taliban ta kwace mulki a cikin watan Augustan da ya gabata wata kungiyar ta masu tsatsaurar ra'ayin kishin Islama ta EIK ke dada kai hare-hare a kan 'yan kabilar na Hazaras wadanda take zargi da kasancewa 'yan bidi'a.
Akalla mutane shida ne suka mutu a wasu jerin hare-haren bamai-bamai a wata makarantar yara da ke a birnin Kabul.