Harin Amurka a Somalia ya hallaka mayakan ISIS

Shugaba Trump wanda ya ce an kashe wasu manyan mayakan da kuma lalata maboyarsu, ya kara da cewar Amurka ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen murkushe duk wata kungiya da ke zama barazana a garesu.

Duk da cewar mayakan ISIS a kasar ta Somalia ba su da yawa kamar mayakan al-Qaeda, sai dai suna daga cikin manyan kungiyoyi masu ikirarin jihadi da suka bulla tun a shekarar 2010.

A baya Amurka ta sha kaddamar da hare-hare a Somalia, musamman a shekarar da ta gabata da nufin kawo karshen ayyukan mayakan masu ikirarin jihadi.

Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohammed ya mika sakon godiya ga Washington biyo bayan harin da ya ce a ci gaba da kai irin sa zai taimaka wajen fatattakar mayakan daga kasarsa.  

Karin Bayani:Sojojin Somaliya sun murkushe 'yan bindiga


News Source:   DW (dw.com)