An halaka daya daga cikin dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya yayin da wasu uku suka jikata, sakamakon ta'addancin kan jerin gwanon dakaru a yankin Kidal na arewacin kasar Mali. Majalisar ta ce lamarin ya ritsa da dakarun kasar Jodan da ke cikin tawogar kiyaye zaman lafiyar.
A cikin wata sanarwa jadakan musamman na Majalisar Dinkin Duniyar a kasar ta Mali da hukumar kula da dakarun kiyaye zaman lafiyar sun ce dakarun sun mayar da wuta kan maharan amma daga bisani daya daga cikin sojojin ya rasa ransa.
Tun shekara ta 2013 kimanin shekaru 10 da suka gabata aka tura dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya zuwa kasar ta Mali da ke yankin yammacin Afirka lokacin da tsageru masu ikirarin jihadi suka yi yunkuri karbe madafun ikon kasar. Akwai kimanin dakarun 13,000 da suke aikin na wanzar da zaman lafiya.