Harbe-harben manyan makamai na sa mutune tserewa daga Goma

Harbe-harben manyan bindigogi na ci gaba da wakana a tsakiyar Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, kwana guda bayan da mayakan kungiyar tawaye ta M23 da ke da goyon bayan Ruwanda suka kwace birnin a hannun dakurun gwamnati. 'Yan jarida na kanfanin dillacin labaran AFP suka ce sun ji karar fashewar bama-bamai da dama, amma kakakin gwamnatin kwango Patrick Muyaya a wata sanarwa da ya wallafa a kafar X, ya ce gwamnati na ci gaba da aiki don gujewa kashe-kashe da asarar rayuka.

Karin bayani: 'Yan tawayen M23 sun yi ikirarin kwace birnin Goma da ke gabashin Kwango

Wannan rintsabewar fada da tabarbarewar diflomasiyya tsakanin DR Kwango da Ruwanda, ya sa gwamnatin Kenya yin kiran taro tsakanin Shugaba Tshisekedi na Kwango da Kagame na Ruwanda cikin kwanaki biyu don gano bakin zaren warware rikicin da aka kwashe sama da shekaru uku ana yi. Fadar mulki ta Kinshasa ta zargi Ruwanda da son kwace arzikinta na karkashin kasa da ke kan iyaka, wanda Kigali ta musanta.

 


News Source:   DW (dw.com)