A cewar rahotannin da ofishin shugaban kasar Ukraine Volodmyr Zelensky ya fidda na nuni da cewar sama da rokoki 120 Rasha ta harba a kusa da tashar nukiliyar da ke kudancin kasar.
A yayin da Ukraine ke zargin Rasha da harba wadannan makamai ita ma a nata bangaren Rasha na nunawa ukraine yatsa. Wannan mataki na kai hari a wannan tashar na nuna girman barazanar da ke tattare da fashewar makaman nukiliya wanda ke da matukar hadari.
Shugaba Volodmyr Zelensky na mai kira ga shugabannin kasashen yamma da su duba yiwuwar karin takunkuman da za su dakatar da Rasha a ci gaba da daukar irin wannan mataki.