Shugaban kungiyar ta Hamas da ke zirin Gaza Yahya Sinwar ya ce kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen lalata dubban wuraren ibadun Yahudawa a fadin duniya, muddin aka ci gaba da dauki ba dadi a masallacin Al-Aqsa.
A makwannin baya-bayan nan dai takaddama ta yi ta barkewa tsakanin Falasdinawa da jami'an 'yan sandan Isra'ila a harabar masallacin, lamarin da kasashen Musulmai ke tir da yadda jami'an ke harba hayaki mai sa hawaye kan Falasdinawan.
Idan har ba a kawo karshen takaddamar ba, kungiyar Hamas dai ta yi barazanar harba rokoki kan Isra'ila a karshen watan Mayun wannan shekarar, a lokacin da Israila ke bikin tunawa da mamaye birnin na Kudus.
Rikicin na baya-bayan nan na haifar da fargabar sake barkewar mummunan rikici makamancin na shekarar bara da aka kwashe tsawon kwanaki 11 ana gwabza yaki tsakanin Isra'ila da kungiyar ta Hamas.