Hamas ta saki bidiyon 'yar Isra'ila da ake garkuwa da ita

Reshen kungiyar Hamas mai dauke da makamai al-Qassam Brigades ya saki bidiyon daya daga cikin Isra'ilawa da 'ya'yan kungiyar suka yi garkuwa da su a harin watan Oktoban 2023.

Bidiyon da aka sake a ranar Asabar mai tsawon minti uku da rabi da kamfanin dillancin labarai na AFP bai tantance sahihancinsa ba, ya nuna wata soja mai shekara 19 ta na neman agaji.

Adadin mutane da Isra'ila ta kashe a Gaza ya dara dubu 45

Liri Albag ta yi magana cikin  harshen Hebrew inda ta bukaci gwamnatin Isra'ila ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an kubutar da ita.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da rahotanni ke cewa ruwan wutan da Isra'ila ta yi a sassa daban-daban na Gaza ya kashe akalla mutum 30 a ranar Asabar.

Isra'ila ta haramta ayyukan UNRWA

Har ila yau, gwamnatin shugaba Biden na Amurka ta sanar wa majalisar kasar cewa za ta sayar wa Isra'ila makamai na dala biliyan takwas domin kare kanta.


News Source:   DW (dw.com)