An mika gawarwakin ga kungiyar agaji ta Red Cross a Khan Younis. A sakon da ya wallafa a shafin X, Shugaban kasar Isra'ila Isaac Herzog ya bayyana bakin cikin ganin an sakon wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da rai ba, a gefe guda jama'a sun yi dandazon don girmama gawarwakin da aka mika cikin akwatuna, za a fara kai gawarwakin cibiyar Nazarin Magunguna ta Isra'ila don tantancewa.
A mako mai zuwa ne za a mika wasu gawarwaki hudu a cewar Hamas. Sannan kuma za a sako wasu mutane shida da aka yi garkuwa da nan gaba.