'Yansanda a Yuganda, sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 11 ciki har da wasu kananan yara a wani wuri da ke wajen Kampala babban birnin kasar, sakamakon fashewar wata tankar da ke shake da man fetir.
Shaidu sun ce tankar da fari ta yi hadari ne inda ta tuntsura, inda daga bisani kuma ta kama da wuta.
'Yansandan sun kuma ce mutanen da hadarin ya rutsa da su sun kone kurmus.
Wasu hotunan bidyo ma dai sun nuno yadda mutanesuka yi ribibin kwasar ganimar man da ke malala daga tankar a lokacin da ta fadi, kafin daga bisani ta yi bindiga.
A makon jiya ne kuma aka samu makancin wannan hadari na motar dakon mai a Jigawa da ke arewacin Najeriya, inda sama da mutum 140 suka rasa rayukansu.