Hatsarin ya faru ne a yayin da mazauna yankin suka yi dandazo kan tankar man don dibar ganima, lamarin da ya haifar da gobarar wasu karin motocin da ke ajiye a kusa da wurin da fashewar ta auku.
Tuni shugaban gwamnatin rikon kasar da ke birnin Tripoli Abdelhamid Dbeibah, ya nuna kaduwa kan hatsarin, tare da bayyana cewa gwamnatin tarayya na bin lamarin sau da kafa.
Tuni aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa wani asibitin da ke birnin Sabha, mai tazarar kilomita fiye da 700 daga birnin Tripoli don yi musu magani.