Hadarin tankar mai ya halaka mutane 14 a arewacin Najeriya

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 14 a wannan Lahadin, sanadiyyar taho mu gama da motar bas ta yi da tankar dakon mai a kauyen Kusobogi mai nisan kilomita 80 da Minna babban birnin jihar Niger.

Kwamandan hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC shiyyar jihar Niger Kumar Tsukwan, ya sanar da cewa motar fasinjojin ce da ta taso daga Lagos za ta je Kaduna, ta gabzawa tankar man, a kokarin da direbanta ke yi na ganin ya wuce wata bas din.

Karin bayani:Fashewar tankar mai ta haddasa mace-mace a Jigawa

Ko a makon da ya gabata mutane 23 ne suka mutu sanadiyyar hadarin babbar motar daukar kaya a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Kididdigar hukumar FRSC ta nuna cewa a shekarar 2024 da ta gabata an samu hadura 9,570, wanda ya halaka mutane 5,421.


News Source:   DW (dw.com)