Hadarin mota a Masar ya hallaka gomman mutane

Hadarin wanda rahotanni suka ruwaito motar ta kwace daga hannu direba kafin daga bisani ta kuma fada a dayan hannu da motoci ke tafiya ya auku ne sakamakon gudu mara kima da direban ke yi.

Kasar masar kamar wasu kasashen Afrika na fama da yawaitar hadarin mota akai-akai wanda ake alakanta shi da rashin kyawun hanya da ma rashin kula daga bangaren dirobobin.

Shekara guda ke nan a watan Oktoban bara wasu motoci makare da fasinjoji suka yi taho mu gama a wata babbar hanya da ke Cairo lamarin da nan take ya hallaka mutane sama da 30.

Karin Bayani: Hadarin mota fitina ga rayuwar dan Adam

 


News Source:   DW (dw.com)