Habeck ya gargadi Ellon Musk kan zaben Jamus

Mataimakin shugaban gwamnatin Jamus Robert Habeck ya yi wannan gargadin ne a wata hira da ya yi da Mujallar Spiegel, bayan da aka tambaye shi ko Musk na zaman barazana ga kasarsa a zaben watan Fabarairu mai kamawa. Musk da ya yi fice wajen yin rubutun tunzuri a shafinsa na X ya jima yana tayar da zaune tsaye a siyasar Jamus, inda a karshen makon da ya gabata ya ayyana goyon bayansa karara ga jam'iyyar AfD mai tsananin kishin kasa da kyamar baki a zaben kafin wa'adi da za a gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairun da ke tafe a Jamus din.

 

 


News Source:   DW (dw.com)