Gwamnatin rikon kwarya a Mali ta kama dan Adawa

Gwamnatin rikon kwarya a Mali ta kama dan Adawa
Hukumomi a Mali sun kama wani kusa a kwancen 'yan adawa bisa zargin dakarun sojin kasar da kisan fararen hula.

Hukumomi a Mali sun kama wani kusa a kwancen 'yan adawar kasar bayan da ya zargi dakarun tsaron kasar da aikata kisan gilla kan fararen hula.
 
Ana zargin Oumar Mariko da furta kalaman ne a yayin wani taron da jam'iyyarsa ta gudanar a makon jiya a birnin Bamako, inda a ciki ya fito karara ya zargi kisan gilla a yankin Moura, yankin da dakarun tsaron kasar suka ce sun halaka mayakan jihadi fiye da 200. 

Tun daga farko dai manyan kasashen duniya irinsu Faransa da Amirka da ma Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci da a gudanar da kwakwaran bincike kan ikrarin Mali na kisan mayakan jihadi, bayan da aka zargi sojan tare da tallafin dakarun Wagna na Rasha da yi wa fararen hula kisan gilla maimakon kakkabe mayakan jihadi.
 


News Source:   DW (dw.com)