Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz ya shaida wa ma'aikatan Meyer Werft kamfanin kasar da ya kware wajen kera jiragen ruwa cewa gwamnatin kasar ta Jamus tana shirye ta tabbatar da cewa kamfanin ya ci gaba da aiki wajen samar da kudin da ake bukata na ceton kamfanin da ke cikin matsalolin kudi. Jagoran gwamnatin ya ce kasar wadda take matsayi na uku na karfin tattalin arziki tsakanin kasashen duniya za ta tabbatar da ci gaba da taka rawa a bangaren sufurin jiragen ruwa a duniya, kuma kamfanin Meyer Werft yana da rawar da zai ci gaba da takawa.
Kamfanin Meyer Werft ya kware wajen kera jiragen ruwa inda ya kwashe fiye da shekaru 200 yana kera jiragen ruwa masu inganci da na alfarma. Tuni gwamnati da bankuna suka fara duba hanyar fitar da wannan shahararren kamfanin kera jiragen ruwa daga cikin matsalolin tattalin arziki da ya samu kansa.
Duk matakin da aka amince game da yadda gwamnati za ta taimaki kamfanin sai ya samu amincewar majalisar dokokin kasar ta Bundestag da hukumar Tarayyar Turai. Kamfanin ya samu koma-baya sakamakon annobar cutar corona wadda ta janyo soke wasu shirye-shiryen kera wasu jirage da aka amince. Yanzu dai gwamnatin Jamus za ta taimaki kamfanin ya samu bashin makuden kudi domin ci gaba da aiki.