Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya gayyaci manyan shugabannin kamfanonin sarrafa karafa da 'yan kasuwa da ma'aikata da kungiyoyin kwadago, don ganawa da su ranar Litinin mai zuwa, domin tattauna hanyoyin magance matsalolin tattalin arziki da kasar ke fuskanta.
Karin bayani:Ma'aikatan kamfanin kera motoci na Volkswagen na yajin aiki
Sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X ta ce tattaunawar za ta mayar da hankali wajen lalubo hanyoyin habaka kamfanonin sarrafa karafuna da kasar ta shahara a kai shekara da shekaru, da bunkasa masana'antu da lantarki da zuba jari, tare da kare kasar daga zama cibiyar jibge tarkacen karafa.
Karin bayani:Scholz ya ba da sanarwar sabon taimako ga Ukraine
A cikin watan Nuwamban da ya gabata ne babban kamfanin mulmula karafa mafi girma na Jamus ThyssenKrupp mai ma'aikata dubu ashirin da bakwai, ya sanar da shirinsa na korar ma'aikata dubu goma sha daya daga nan zuwa shekaru 6 masu zuwa, lamarin da ya sanya Mr Scholz nuna damuwa a kai.