Kwamishinan lafiya na jihar Borno Farfesa Baba Malam Gana shi ne ya sanar da barkewar cutar ta kwalara, inda ya ce mutane 451 ne suka kamu da wannan cuta a kananan hukumomin Jere da Mafa da Konduga da Dikwa da karamar hukumar birnin Maiduguri da ke murmurewa daga ibtila'in ambaliyar ruwa da ya yi sanadiyyar rayuka.
Karin bayani: Ambaliyar ruwa: Dabbobi da dama sun mutu a Borno
Tun kafin barkewar wannan cuta ta amai da gudawa a jihar, masana kiwon lafiya har ma da hukumomin kasa da kasa sun yi gargadin bullar cututtuka da dama sakamakon gurbacewar ruwan amfanin yau da kullum da dagwalo bayan ambaliyar ruwa.