'Yar uwar shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un ta siffanta ministan tsaron Koriya ta Kudu da mutum mai ''kalamai marasa ma'ana''.
Kim Yo Jong na mayar da martani ne a wannan Lahadi biyo bayan kalaman ministan Koriya ta Kudun Kim Suh Wook, a game da yawaitar gwajin makamai masu linzami da gwamnatin Koriya ta Arewa ke yi a wannan shekara.
Masana dai na siffanta wannan kalaman da cewa akwai yiwuwar Koriya ta Arewa wadda kasashen duniya ke nuna fargabar a kan makamanta na nukiliya, ta ci gaba da yin gwajin makamai masu linzamin da kusan kowane lokaci ke razana makwabciyarta, Koriya ta Kudu.