Guterres zai zo Afirka bikin Karamar Sallah

Guterres zai zo Afirka bikin Karamar Sallah
A yayin ziyarar tasa, Guterres, zai yi buda baki da Shugaban Senegal Macky Sall sannan zai gana da Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar da kuma Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya.

Sakatare Janar na MDD, Antonio Guterres, ya shirya kawo ziyara a kasashen Afirka ta Yamma domin yin shagulgulan Karamar Sallah da mabiya addinin Islama albarkacin kammala azumin watan Ramadan.

Sanarwar da MDD ta fitar ta nuna cewa Guterres zai isa kasar Senegal a wannan Asabar. A ranar Litinin kuma zai je Jamhuriyar Nijar, sai kuma Najeriya da sakatare janar din zai ziyarta a ranar Talata kafin ya koma ofishinsa da ke Amurka.

Ziyarar ta  Guterres za ta ba shi damar ganawa da kungiyoyin sa kai da na addinai da kuma iyalan mutanen da rikici ya tagayyara a kasashen Sahel, inda zai duba yadda zuwan coronavirus da sauyin yanayi suka shafi rayuwar marasa galihu.


News Source:   DW (dw.com)