Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce barazana da makaman nukiliya ta sake dawowa bayan samun saukin hakan tsawon shekaru da dama.
Mr. Guterres na fadin haka ne lokacin wani taron manema labaru da ya yi a birnin Tokyo na kasar Japan.
Wannan dai wani martani ne ga hari da aka kai wa tashar makamashin nukiliya mafi girma a nahiyar Turai ta Zaporizhzhya da ke Ukraine.
Jagoran na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce dole ne kasashen duniya su kiyaye amfani da muggan makaman na nukiliya wanda ga dukkan alamu ake kokarin isa gare su saboda hadarin su.
Antonio Guterres dai ya je kasar ta Japan ne domin halartar taro karo na 77 na tunawa da harin da Amirka ta kai da makamin nukiliya a Hiroshima a lokacin yakin duniya na biyu.