A lokacin tattaunawarsa da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, Mista Guterres ya ce ba abin da ke gabansu illa samar da yanayin tattaunawar tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Ukraine.
Bayan ganawarsa da Lavrov, Mista Guterres zai samu tarba daga shugaba Vladimir Putin na Rasha. Daga bisani kuma ya zai je kyiv babban birnin Ukraine, inda yake shan kakkausar suka daga shugaba Volodymyr Zelensky dangane tsarinsa na fara zuwa Rasha, lamarin da ya ce "babu adalci" a cikinsa.
Tun bayan kutsawar Rasha a Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu, Majalisar Dinkin Duniya ta zama saniyar ware a wannan rikici, sakamakaon rarrabuwar kawuna tsakanin kasashe biyar masu kujerun dindindin a Kwamitin Sulhun, wanda Rasha ke cikin su.