Gumurzu tsakanin sojan Nijar da Lakurawa

A cewar mazauna kusa da yankin, tun daga safiyar wannan Laraba ake ta jin karar bindigogi, musamman kusa da wasu makarantun boko wadanda 'yan bindigar suka auka wa dakarun da ke sa'ido kan bututun man da ya ratsa yankin. An dai share sa'o'i motocin sufuri na dakon a saki hanyar domin basu sukunin wucewa. Saidai duk da cewar ba a samu cikakken adadin wadanda suka mutu ba, amma rahotanni daga yankin sun bayyana cewar an ga gawarwakin 'yan bindigan da dama a kan hanya, wadanda sojojin suka samu nasarar ganin bayansu. A cewar wakilin DW a yankin Isoufou Mamane, yankin na birnin Konni da ke kan iyaka da Najeriya da Nijar inda sabuwar kungiyar ta Lakurawa ta kafa sansaninta, tun lokacin yake fuskantar hare-hare daga 'yan bindigar. Wannan dai shi ne hari na biyu a kasa da wata guda da mayakan Lakurawan ke kawo wa yankin na Konni.


News Source:   DW (dw.com)