Guinea: Zanga-zangar adawa da mulkin soji

Guinea: Zanga-zangar adawa da mulkin soji
'Yan sanda a Guinea Conakry sun yi amfani da kulake da barkonon tsofuwa wajen tarwtsa dubban jama'a da suke yi zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin mulkin soji.

A unguwanni da dama  na Conakry babban birnin kasar an yi arangama tsakanin 'yan sandar da matasa wadanda suka datse hanyoyin da shingaye tare da kona tayoyi.Yanzu haka an ce an kashe mutum daya sai dai hukumomi ba su tabbatar ba. Hadin gwiwar jam'iyyu, siyasar da kungiyoyin kwadago da na farar hula da ke fafutukar ganin an sake mayar da kasar bisa turba dimukaradiyya suka tshirya gangamin. Kanar Mamadou Doumbouya wanda ya hambarar da gwamnatin Alpha Conde daga kan karagar mulki a cikin watan Satumba bara, ya sha alwashin mika mukli ga farar hula cikin shekaru uku, sai dai kungiyoyin sun ce sojojin ba su da niyya.

 


News Source:   DW (dw.com)