Guinea za ta ci gaba da hana zanga-zanga

Guinea za ta ci gaba da hana zanga-zanga
Gwamnatin mulkin sojan Guinea ta yi watsi da bukatar Majalisar Dinkin Duniya kan dage hana zanga-zanga.

Gwamnatin mulkin sojan kasar Guinea ta yi watsi da bukatar Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar mata kan dage hana zanga-zangar siyasa a kasar, inda gwamnatin take cewa zanga-zanga da gangami za a yi ne kadai lokacin zabukan da aka tsara cikin shekaru uku da ke tafe. Tun farko hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta nemi ganin sojoji sun cire haramcin zanga-zangar.

A watan Satumba sojoji suka kifar da gwamnatin Shugaba Alpha Conde sannan daga bisani sojojin suka haramta duk wata zanga-zanga gabanin shirin mayar da kasar bisa tafarkin dimukaradiyya.

Tun lokacin da Kanar Mamady Doumbouya ya kwace madafun ikon kasar ta Guinea da ke yankin yammacin Afirka yake takun saka da kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS wadda ta bukaci komawa tafarkin dimukaradiyya cikin hanzari a kasar.

 


News Source:   DW (dw.com)