Goma: An cinna wa ofishin jakadancin Faransa wuta a DRC

An kaddamar da hari kan ofishin Jakadancin Faransa da ke Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da safiyar Talata.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ne tabbatar da kai harin, tare da cewa ofishin ya kama da wuta amma an yi nasarar kasheta ya zuwa yanzu.

Ministan ya ce sam ba za a lamunci irin wannan farmakin ba kuma Faransa ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da babu abinda ya samu ma'aikatan ofishin jakadancin nata.

Mutane na ficewa daga garin Goma

A wata sanarwa da ya wallafa a shafin X mista Barrot ya ce kasarsa za ta yi duk abinda ya kamata wajen kare Faransawa dake Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

Ana  ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin mayakan M23 da ake zargi na samun goyon bayan Rwanda da kuma sojojin DRC a birnin Goma mai dumbin ma'adinan kasa.

An rika ganin gawarwaki yashe a gefen tituna da jin karar harbe-harbe a yayin da asibitoci suka cika makil a ranar Talata a birnin na Goma a gabashin DRC.

Rikicin Jamhuriyar Kwango da Ruwanda ya yi kamari

An shiga wannan rudanin ne biyo bayan kwace birnin da 'yan tawayen M23 da ake kyautata zaton na samun goyon bayan Rwanda suka yi a jiya Litinin.

A daya bangaren kuwa sojojin gwamnatin Kongo da sauran mayakan da ke mara musu baya na kokarin sake karbe iko da birnin tare da korar M23 da ga yankunan da suka kama.

Masu zanga-zanga kuwa a birnin na Goma sun cinna wa ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ofisoshin jakadancin Rwanda da Faransa wuta inda suke zargin akwai hannun kasashen a cikin abinda ke faruwa.

Wannan hali da birnin Goma ya shiga shi ne mafi muni tun a 2012, kuma rikicin ya faro ne shekara talatin da suka gabata tun bayan yakin kare dangin Rwanda.


News Source:   DW (dw.com)