Sama da mutum 100 ne suka salwanta sakamakon fashewa da aka samu a wata matatar mai ta bayan fage a yankin Abaezi Ohaji-Egbema cikin jihar Imo da ke a kudu maso gabashin Najeriya.
Lamarin ya faru ne cikin daren ranar Asabar kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan jihar Michael Abbatam ya sanar, kuma mutanen da hadarin ya shafa dai sun kone ne kurmus.
Rashin ayyukan yi da tsananin talauci a yankin Neja Delta mai arzikin mai, ya sanya mutane da dama shiga aikin tace mai ta bayan fage a kudancin Najeriya.
Harkar da ta yi kamari a Neja Delta da ke cikin jihar Ribas, na kunshe da hadari kwarai da gaske.
Ko cikin watan Oktobar bara ma dai wata fashewar a wata matatar ta salwantar da mutum 25 a jihar ta Ribas.
Cikin watan Fabrairun da ya gabata, hukumomin yankin suka ce suna daukar matakan rufe irin wadannan matatu na bayan fage.