Hukumomi a kasar Bangladesh sun tabbatar da mutuwar muitane 49 a sakamakon ibtil'ain gobarar da ta barke a wurin aje kayayaki Kudu maso gabashin kasar. Masu aikin ceto sun ce ko baya ga wadanda suka mutu akwai akalla mutun 300 ne suka jikkata.
Ana kuma hasashen alkaluman farko da aka bayar na wadanda suka mutun ka iya karuwa ciki har da 'yan jarida da jami'an kwana-kwana, bayan da aka hakikance bakwai daga cikin mamatan.
Wasu ganau sun ce sun hango gawarwaki da dama warwatse, kana tuni ma dai hukumomin tsaro suka girke soji akalla 250 don ci gaba da aikin ceto. Ana zargin wasu kwantinoni da ke shake da sinadarai a Sitakunda a matsayin wadanda suka hadasa gobarar.