Gobara ta kashe mutane 66 a Turkiyya

Akalla mutane 66 suka rasu wasu mutum 50 kuma suka sami raunuka a wata gobara da ta tashi a wani otel a wurin shakatawa a arewa maso yammacin Turkiyya.

Gobarar ta tashi ne a wurin cin abinci na ginin mai hawa goma sha biyu da ke kan tsaunin Kartalkaya da misalin karfe uku da miniti 27 na dare.

Wasu daga cikin mutanen da lamarin ya ritsa da su sun rasu ne bayan da suka yi tsalle suka diro daga kan benen mai hawa goma sha biyu cikin firgici.

 


News Source:   DW (dw.com)