Gobara ta faru ne a sakamakon dameji da wutar lantarkin asibitin ta yi,wanda nan da nan dakunan asibitin suka kama da wuta. Gwamnan yankin Demba Diop ya ce an yi kokarin ceto jarirrai guda uku. Shugaba Macky Sall,wanda yanzu haka yake yin rangadi a cikin kasashen waje, ya wakilta ministansa na harkokin cikin gida zuwa birnin na Tivaouane cibiyar 'yan darikar Tijaniya domin isar da ta'aziyarsa.