Girgizar kasa mai karfin maki 6.4 ta far wa Taiwan

Wata girgizar kasa mai karfin maki 6.4 ta far wa yankin nan mai duwatsu a birnin Chiayi dake kudancin Taiwan a cewar rahotanni.

Girgizar ta jijjiga gine-gine a babban birnin kasar Taipei kuma ta tona ramin da zurfinsa ya kai kilomita 9.4 ko da yake ba ta yi mummunar barna ba.

Guguwa mai karfin gaske ka iya afkawa Taiwan

Hukumar kashe gobara ta kasar ta ce mutum biyu sun samu raunuka sannan ta kuma lalata gine-gine a birnin Tainan.

Taiwan na daga cikin kasashen duniya da ke fama da girgizar kasa lokaci zuwa lokaci lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiya.

Chaina ta kaddamar da sabbin atisayen soji a kusa da Taiwan

A shekara 2016 mutane sama da 100 sun  rasu a wata girgizar kasa a kudancin Taiwan, sannan a 1999 girgizar kasar ta halaka sama da mutane 2,000.


News Source:   DW (dw.com)