Girgizar kasa mai karfin maki 5.8 a ma'aunin Richter ta afka wa kasar Habasha a wannan Asabar, inda ta haddasa manyan ramuka a yakunan da ke da nisan kilomita 142 da Addis Ababa babban birnin kasar, ko da ya ke babu karin haske daga hukumomin kasar kan irin barnar da ta haddasa zuwa yanzu.
Karin bayani:'Yan rakiyar Amarya 71 sun mutu a Habasha
Cibiyar bincike da nazarin al'amuran da suka shafi karkashin kasa ta Amurka USGS, tare da takawarta ta Jamus GRCG ne suka tabbatar da faruwar ibtila'in, inda suka ce zurfin ramin da girgizar kasar ta haddasa ya kai nisan kilomita 10.
Karin bayani:Habasha : Shekaru 40 da kafa gidauniyar yaki da yunwa
Ko a ranar Juma'a an fuskanci girgizar kasar mai karfin maki 5.5 a ma'aunin Richter a Habasha, tare da motsin kasa sama da 30 a sassa dabam-dabam na kasar a cikin makon.