Alkaluman sakamakon da hukumar zaben ta fitar a farko ya nuna jam'iyya mai mulki ta Georgian Dream Party na kan hanyar lashe zaben da gagarumin rinjaye inda ta sami kusan kashi 54 cikin dari na kuri'iun da aka kada.
Sakamakon ya kuma nuna kawancen Jam'iyyu hudu na adawa sun sami kashi 38 cikin dari na kuri'un
Jam'iyyun adawar dai da kuma shugabar kasar Salome Zourabichvili wadda ta yi kaurin suna wajen sukar lamirin gwamnatin Firaminista Irakil Kobakhidez sun ce an tafka magudi.
Dubban jama'a sun fita titunan Tbilisi don nuna fushinsu da sakamakon zaben.