Gaza: Yarjejeniyar tsagaita wuta na tangal-tangal

A wannan Lahadin ce yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da Hamas za ta fara aiki da kuma sakin wadanda aka yi garkuwa da su, matakin da ake ganin zai bude kofar kawo karshen yakin da aka kwashe watanni 15 ana gabzawa a Gaza. Tuni dai dakarun Isra'ila suka fara janyewa daga yankunan Rafah na Gaza zuwa wata hanya da ke kan iyakar Gaza da Masar.

To sai dai kuma Firanministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi gargadin cewa, yarjejeniyar ba za ta fara aiki a lokacin da aka tsara ba face Hamas ta bayyana sunayen wadanda za ta saki. Ana ta martanin, kungiyar Hamas ta ce ta samu tsaikon sakin sunayen ne sakamkon matsalolin na'ura.

Karin bayani: Isra'ila ta yi na'am da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Yarjejeniyar tsagaita bude wutar ta biyo bayan kwashe tsawon watanni takwas ana kai ruwa rana a shiga tsakani da kasashen Masar da Qatar da kuma Amurka suka yi. Matakin farko na yarjejeniyar zai yi aiki ne a na tsawon makwanni shida, a wannan lokacin za a mikawa Isra'ila mutane 33 daga cikin 98 da Hamas ta yi garkuwa inda za a yi musayar su da Falasdinawaa fiye da 1900 da ke zama fursononi a Isra'ila.

 


News Source:   DW (dw.com)