Kimanin mutum dubu uku da dari biyar ne suka shiga wani gagarumin gangami, don jan hankalin shugabanin kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 da ke shirin soma taron kolinsu a gobe Lahadi a Jamus. Kungiyoyi dabam-dabam da suka hada da masu rajin kare muhalli da dabbobi da masu rajin kare hakkin bil'adama na son taron na jahar Bavariya, ya mayar da hankali wajen rage hayaki mai gurbata iska da ke kuma haifar da barazanar bacewar hallitun cikin ruwa da kuma uwa uba daukar matakan ceto duniya daga matsananciyar yunwa.
Daga cikin masu gudanar da gangamin, da dama sun yarda cewa, idan har shugabanin kasashen na G7, za su kokarta su inganta iskar da ake shaka da magance sauyin yanayi, to hakan zai taimaka a magance matsalolin da ka iya zama illa ga rayuwar al'ummar duniya.